Connect with us

LATEST

Jam’iyyar APC ba za tayi nasara a 2019 ba Inji Gwamna Dickson

Published

on

– Gwamnan Jihar Bayelsa yace Jam’iyyar APC ba za ta ci zaben 2019 ba

– Seriake Dickson yace yanzu babu abin da ake yi a APC sai rikici iri-iri

– Yace ko lokacin da Jam’iyyar ke da karfi ba ta iya nasara a Bayelsa ba

 

Gwamna Henry Seriake Dickson ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta shiga cikin rudu iri-irin don haka ma yace ko kadan babu yadda za ayi Jam’iyyar mai mulkin kasar tayi nasara a zaben 2019.

Gwamna Dickson yace Bayelsa ta fi karfin Jam’iyyar APC Henry Seriake Dickson ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa Fidelis Soriwei yace APC ba za ta iya lashe zabe mai zuwa ba. Gwamnan ya bayyana wannan ne lokacin da yake jawabi a Garin Yenagoa a Jihar Bayelsa.

KU KARANTA: An ceto wasu da ke hannun Boko Haram a Najeriya Gwamnan ya nuna cewa Jam’iyyar APC tana cikin rudu ne a yanzu inda rikicin yau dabam kuma na gobe dabam. Gwamna Dickson yace wasu ‘Yan APC da-dama yanzu su na dawowa jirgin Jam’iyyar PDP a Jihar sa domin su tsira.

A cewar Gwamnan dai ko a lokacin zaben 2015, Jam’iyyar APC ba ta iya yin nasara a Jihar Bayelsa ba duk da cewa kuwa Jam’iyyar ke rike da kasar. Gwamnan yace alkawuran karya kurum APC ke yi wa mutane kuma ba za su kai labari ba.

Sai dai Gwamnan yace ana kokarin kakkabe takardun Ma’aikatan Jihar Bayelsa domin karawa wasu matsayi wanda hakan ya jawo koke-koke daga mutanen Jihar sa. Gwamna Dickson yace shi ma bai ji dadin yadda hakan ya kasance ba.

KARANTA KUMA  Jerin sabbin shugabannin jam'iyyar APC 11 da aka zaba tare da Oshiomhole a jiya

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Entertainment

Ko a yau aka gudanar da Zaɓe za muyi nasara – APC

Published

on

By

Yunƙurin jam’iyyar adawa ta PDP na fakewa ƙarƙashin sabuwar dokar nan ta zabe da ke tsimayin sahalewa a kasar nan wani ƙoƙari ne na kawar hankalin al’umma daga al’amurran shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki na rashin amincewa da zaman majalisa domin tattauna batutuwan kasafin kudin zaben 2019.

Rashin amincewar Saraki na katse hutun majalisar sa domin gudanar da muhimmin zama na tattauna al’amurra tare da amincewa da tanadar kasafin kudin aiwatar da zaben 2019 wata kitimurmura ce kamar yadda jam’iyyar APC ta bayyana.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kakakin jam’iyyar APC, Mista Yekini Nabena, ya bayyana wannan zargi cikin birnin Abuja da cewar Saraki na fakewa ne kurum da wannan tuggu domin ci gaba da tsawaita hutun da majalisar sa ta shiga makonni da suka gabata.

Ya ci gaba da cewa, duk da irin wannan tuggu da jam’iyyar PDP ke ci gaba da kullawa ba zai hana jam’iyyar APC samun nasara zaben 2019 koda kuwa a yanzu za a gudanar da shi.

Jam’iyyar ta APC ta bayyana fushin ta dangane da yadda Shugaban majalisar dattawa ke samun goyon bayan jam’iyyar sa ta PDP wajen gudanar da mulkin na isa tare da janyo nakasu gami da barna ga shugabancin kasar nan musamman ga hukumar zabe ta kasa watau INEC.

Kazalika jam’iyyar ta yi kira ga dukkanin masu kishin kasar Najeriya akan su nemi hakkokin su ta hanyar furuci da baka domin tabbatar da majalisar dokoki ta tarayya ta sauke nauyin kundin tsarin mulkin kasa da ya rataya a wuyan ta.

 

KARANTA KUMA  Jerin sabbin shugabannin jam'iyyar APC 11 da aka zaba tare da Oshiomhole a jiya

 

Continue Reading

LATEST

Yanzu-yanzu: Tambuwal ya fita daga APC, ya koma PDP

Published

on

By

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress APC, zuwa Peoples Democratic PArty PDP da ranan yau Laraba, 1 ga watan Agusta 2018.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a wata hira manema labarai a gidan gwamnatin jihar Sokoto. Ya yi wannan sanarwa ne cikin daruruwan magoya bayansa da suka yi dandazo a gidan gwamnatin jihar domin nuna goyon bayansu gareshi. Wannan sanarwa ya zo ne bayan makonni da ake hasashe gwamna Tambuwal zai fita daga jam’iyyar APC.

Kwanan nan ya siffanta gwamnatin shugaba Buhari a matsayin wacce ta gaza kuma demokradiyyan gidan yari.

 

Tsohon kakakin majalisar wakilan ne gwamna na uku yanzu da suka sauya sheka daga jam’iyya mai ci zuwa jam’iyyar adawa. Wadanda suka sauya sheka gabanin yau sune gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da Abdulfatah Ahmed na Kwara.

 

KARANTA KUMA  Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2018
Continue Reading

LATEST

Yanzu Yanzu: Tirela ya yi karo da tankar mai a hanyar Suleja-Minna

Published

on

By

Kakakin hukumar kare hatsarurruka a hanya, FRSC, Mista Bisi Kazeem ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne da safe.

Ya kara da cewa jami’an hukumar kashe gobara dad a na FRSC sun kasance a wajen domin kashe wutan yayinda motocin ke konewa.

Ga hotunan a kasa:

Idan ba zaku manta ba a daren ranar Alhamis, 28 ga watan Yuni ne wuta ya tashi a babban titin Lagas zuwa Ibadan inda motoci 54 suka gone, yayinda mutane tara suka mutu, hudu suka ji rauni.

 

KARANTA KUMA  Yanzu-yanzu: Tambuwal ya fita daga APC, ya koma PDP
Continue Reading

Headlines