Connect with us

LATEST

Rikicin APC: Dogara zai jagoranci ‘Yan nPDP su gana da Uwar Jam’iyya

Published

on

Daily Trust ta rahoto cewa an shirya wani kwamiti na mutunae 9 da za ta zauna domin dinke barakar da ake samu tsakanin tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar PDP da ke cikin APC da Uwar Jam’iyyar. Tun kwanaki ‘Yan nPDP su ka aikawa Shugaba Buhari takarda. 

 

A Ranar Litinin mai zuwa ne za a cigaba da zama domin shawo kan karshen banbancin da aka samu tsakanin ‘Yan nPDP da APC. ‘Yan nPDP sun nada Shugaban Majalisar Wakilai Rt. Hon. Yakubu Dogara ya jagorance su wajen zaman da za a fara yi a Ranar Litinin.

Kwamitin da aka shirya ya gana da Uwar Jam’iyyar ya kunshi wasu mutum 4 daga Fadar Shugaban Kasa da APC da kuma mutane 5 daga ‘Yan nPDP. Yanzu dai har an aikawa Shugaban Kasa Buhari sunayen wadanda za a zauna din da su kamar yadda mu ke ji.

Yan nPDP dai sun hada da Shugabannin Majalisar Tarayya da wasu Sanatocin da ‘Yan Majalisu da tsofaffin Gwamnoni da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal. Abubakar Kawu Baraje shi ne Shugaban ‘Yan nPDP kuma yana cikin wadanda kwamitin da aka kafa.

Sauran ‘Yan nPDP da za su gana da manyan da ke Fadar Shugaban Kasar su ne Sanata Danjuma Goje. Bernabas Gemade, da kuma Adamu Aliero.

Bukola Saraki da irin su Sanata Kwankwaso ba su cikin wadanda za su zauna da Uwar Jam’iyyar a makon gobe. Tun tuni dai kun ji cewa Jagororin na nPDP sun koka ne game da yadda aka yi zaben shugabannin Jam’iyyar a Jihohi. Yanzu dai za ayi kokarin dinke duk barakar da aka samu tsakanin tsofaffin ‘Yan PDP da Uwar Jam’iyyar inji Shugaban APC Lawan Shuaibu.

KARANTA KUMA  Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin 2018

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Entertainment

Ko a yau aka gudanar da Zaɓe za muyi nasara – APC

Published

on

By

Yunƙurin jam’iyyar adawa ta PDP na fakewa ƙarƙashin sabuwar dokar nan ta zabe da ke tsimayin sahalewa a kasar nan wani ƙoƙari ne na kawar hankalin al’umma daga al’amurran shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki na rashin amincewa da zaman majalisa domin tattauna batutuwan kasafin kudin zaben 2019.

Rashin amincewar Saraki na katse hutun majalisar sa domin gudanar da muhimmin zama na tattauna al’amurra tare da amincewa da tanadar kasafin kudin aiwatar da zaben 2019 wata kitimurmura ce kamar yadda jam’iyyar APC ta bayyana.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kakakin jam’iyyar APC, Mista Yekini Nabena, ya bayyana wannan zargi cikin birnin Abuja da cewar Saraki na fakewa ne kurum da wannan tuggu domin ci gaba da tsawaita hutun da majalisar sa ta shiga makonni da suka gabata.

Ya ci gaba da cewa, duk da irin wannan tuggu da jam’iyyar PDP ke ci gaba da kullawa ba zai hana jam’iyyar APC samun nasara zaben 2019 koda kuwa a yanzu za a gudanar da shi.

Jam’iyyar ta APC ta bayyana fushin ta dangane da yadda Shugaban majalisar dattawa ke samun goyon bayan jam’iyyar sa ta PDP wajen gudanar da mulkin na isa tare da janyo nakasu gami da barna ga shugabancin kasar nan musamman ga hukumar zabe ta kasa watau INEC.

Kazalika jam’iyyar ta yi kira ga dukkanin masu kishin kasar Najeriya akan su nemi hakkokin su ta hanyar furuci da baka domin tabbatar da majalisar dokoki ta tarayya ta sauke nauyin kundin tsarin mulkin kasa da ya rataya a wuyan ta.

 

KARANTA KUMA  Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kada ya sake tsayawa takara a 2019

 

Continue Reading

LATEST

Yanzu-yanzu: Tambuwal ya fita daga APC, ya koma PDP

Published

on

By

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress APC, zuwa Peoples Democratic PArty PDP da ranan yau Laraba, 1 ga watan Agusta 2018.

Gwamnan ya bayyana wannan ne a wata hira manema labarai a gidan gwamnatin jihar Sokoto. Ya yi wannan sanarwa ne cikin daruruwan magoya bayansa da suka yi dandazo a gidan gwamnatin jihar domin nuna goyon bayansu gareshi. Wannan sanarwa ya zo ne bayan makonni da ake hasashe gwamna Tambuwal zai fita daga jam’iyyar APC.

Kwanan nan ya siffanta gwamnatin shugaba Buhari a matsayin wacce ta gaza kuma demokradiyyan gidan yari.

 

Tsohon kakakin majalisar wakilan ne gwamna na uku yanzu da suka sauya sheka daga jam’iyya mai ci zuwa jam’iyyar adawa. Wadanda suka sauya sheka gabanin yau sune gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, da Abdulfatah Ahmed na Kwara.

 

KARANTA KUMA  Yanzu Yanzu: Tirela ya yi karo da tankar mai a hanyar Suleja-Minna
Continue Reading

LATEST

Yanzu Yanzu: Tirela ya yi karo da tankar mai a hanyar Suleja-Minna

Published

on

By

Kakakin hukumar kare hatsarurruka a hanya, FRSC, Mista Bisi Kazeem ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne da safe.

Ya kara da cewa jami’an hukumar kashe gobara dad a na FRSC sun kasance a wajen domin kashe wutan yayinda motocin ke konewa.

Ga hotunan a kasa:

Idan ba zaku manta ba a daren ranar Alhamis, 28 ga watan Yuni ne wuta ya tashi a babban titin Lagas zuwa Ibadan inda motoci 54 suka gone, yayinda mutane tara suka mutu, hudu suka ji rauni.

 

KARANTA KUMA  “Zan so na sace shi zuwa APC “ –Shugaba Buhari ya na son ganin wani sanatan PDP ya koma APC
Continue Reading

Headlines