“Zan so na sace shi zuwa APC “ –Shugaba Buhari ya na son ganin wani sanatan PDP ya koma APC

Shugaba Buhari, cikin raha da barkwanci, ya bayyana cewar, “zan so na sace mataimakin bulaliyar majalisar dattijai, Philip Aduda, zuwa jam’iyyar APC.” Sanata Aduda mamba a majalisar dattijai ta kasa dake wakiltar birnin tarayya, Abuja, ya lashe zabe ne a karkashin jam’iyyar PDP har sau biyu, 2011 da kuma 2015.

Buhari ya fadi hakan ne yayin da manyan jami’an gwamnati, malaman addini da ,yan siyasa suka kai masa ziyarar gaisuwar sallah a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

“Naga duk da kana jam’iyyar adawa sai kara kiba ka ke, ina ganin a zaben gaba sace ka zamu yi zuwa jam’iyyar APC,” shugaba Buhari ya fadawa Aduda. Sanata Philip Aduda Shugaba Buhari ya nuna farincikin sa bisa yadda adawa bat a hana ‘yan siyasa hada kai domin fafutikar kawo cigaba ga jama’ar Najeriya.

A sakon sa na barka da Sallah, Shugaba Buhari ya yi kira ga musulmi da su dore da halayen kirki har bayan azumin watan Ramadana mai alfarma. Bayan hakan, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su raba addini da tarbiya, domin a cewar sa, yin hakan zai bayar da kafa ga balagurbin shugabanni.

A cikin sakon nasa, ga musulmi, na kammala azumi, shugaba Buhari ya yiwa musulmi murnar ganin watan Ramadana tare da bukatar su zama masu koyi da kyawawan halayen masu azumi domin zama wakilan Musulunci na kwarai.

 

KARANTA KUMA  Komawa APC ba zai cece ku ba – Fadar shugaban kasa tayi ba’a ga barayin yan siyasa

Add comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *