Wani Babban Fasto ya bayyana muhimmin dalilin da ya sa yake matukar kaunar Buhari

Wani babban Faston darikar Methodist na addinin Kirista, Oche Job ya bayyana matukar kaunar da yake da shi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace hakan na karuwa a ransa ne sakamakon halin rashin tsoro da shugaba Buhari ke da shi.

Jaridar The Cables ta ruwaito Faston Job ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuni, inda yace idan Buhari ya yanke shawarar daukar mataki sai ya aiwatar shi, kuma baya tsoron maganganun masu magana.

Majiyar NAIJ ta ruwaito shi yana cewa: “Tabbas, ina yaba masa, kun san Buhari baya tsoro kowa, wannan shi yasa nake sonsa, yana yanke shawarar daukar duk matakin da yake ganin zai amfani yan Najeriya. Kun san ba lallai jama’a su yaba masa ba, amma sai bayan ya bar kujerar ne za’a fara kwantanta shi da wanda zai gaje shi.

Fasto Job ya jinjina ma Buhari da sanya hannu kan dokar baiwa majalisun jihohi cin gashin kansu ta hanyar basu kudadensu kai tsaye ba tare da bin hannun gwamnoni ba, inda yace hakan zai tabbatar da yaki da rashawa.

Daga karshe yayi kira gay an siyasar da suka samu nasara a zabuka da su fara aiki tun kafin a rantsar dasu domin acewarsa kwanakinsu na tafiya ne, ba wai zasu jira su bane har sai sun hau karagar mulki.

KARANTA KUMA  Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

Add comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *