Yanzu-yanzu: An kashe dan sanda 1 yayinda rikici ya barke tsakanin yan Shi’a da yan sanda

An hallaka dan sanda daya har lahira a sabuwar rikici da ya barke tsakanin yan sanda da yan kungiyar Shi’a a zanga-zangan da sukeyi kan cigaba da tsare shugabansu, Sheik Ibrahim Zakzaky.

a da yan kungiyar Shi’a a zanga-zangan da sukeyi kan cigaba da tsare shugabansu, Sheik Ibrahim Zakzaky.

Kakakin hukumar yan sanda a jihar Kaduna, Muktar Aliyu, ya tabbatar da wannan labari da ya faru a yau Alhamis, 1 ga watan Yuni 2018. Game da cewarsa, dan sandan na tafiyarsa a kan hanya kawai sai yyan Shi’an sukayi masa ribiti da caccaka masa wuka har lahira.

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa An rufe manyan hanyoyin zuwa babban kotun jihar Kaduna da safiyar yau Alhamis, 21 ga watan Yuni yayinda ake shirin gurfanar da shugaban kungiyar IMN da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Yan jaridan da suka tafi kotun basu samu daman shiga ba yayinda manyan jami’an tsaro suka tare dukkan hanyoyi domin hana jama’a samun isa harabar kotun. Hakazalika masu abubuwan hawa basu saman daman wucewa ba daga Kabala doki zuwa Indepence way zuwa Waff road

Daga baya, an gaza cigaba da gurfanar saboda rashin halartan Alkalin da ya kamata ya bayar da Shari’a a kotun.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky dai yana gurfana a kotu ne kan laifin tara mabiya ba bisa doka ba, kokarin fito-na-fito da gwamnati.

 

KARANTA KUMA  Gwamnatin Shugaba Buhari ta kware wajen yaudara - Atiku

Add comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *