Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

Nigeria daily times.Com na bada rahoton cewa jirgin shugaba Buhari dauke da shi da wasu mukarrabansa ya dira babban filin jirgin saman Umaru Musa Yar’Adua International Airport Katsina misalin karfe 9:56 na safiyar nan.

Shugaban kasan ya samu tarba ne daga gwamnan jihar, Mal Aminu Bello Masari, da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar.

A nan jihar Katsinan, shugaba Buhari zai karbi bakuncin shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbe Eyadema.

Kana zai kai ziyarar ban girma ga sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumuni Usman, inda zai tattauna da malaman da masu unguwa kan da masu ruwa da tsaki a jihar kan abubuwan da suka shafi cigaban kasa.

Buhari zai yi amfani da wannan dama wajen jajentawa gwamnatin jihar da jama’arta kan annobar mabaliyar da ya afka musu inda mutane 6 suka hallaka kuma akayi hasaran gidaje 530.

KARANTA KUMA  Shehu Sani da Hunkuyi sun fita daga jam'iyyar APC

Add comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *