Dan Allah kada ku fice daga APC – Oshiomhole ga ‘Yan sabuwar APC

Sabon zababben shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya roki fusatattun ‘yan jam’iyya da suka kafa sabuwar APC mai suna gyararriyar APC wato ‘reformed APC’ da su mai da wukar su, sannan su dan bashi lokaci domin shawo kan matsalolin da ke cunkushe a jam’iyyar.

Oshiomhole ya ce: “Ina rokon ku da kuyi hakuri.”

A cewarsa yana so ya basu tabbacin cewa a matsayin sa na sabon shugaban jam’iyyar yanzu, idan aka tunashe shi zai waiwayo ya gyara dukkanin kura-kuran da ake zargin jam’iyyar da tafkawa.

Ya kara da cewa yanzu ne aka zabe su kuma da shi da sauran sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar za su mai da hankali wajen ganin sun gyara kuskuran da aka yi a baya.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa manyan sanatoci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All progressives Congress (APC) sun yi ganawa mai muhimmancin da kwamitin aikin jam’iyyar na kasa. Sun gana ne a ranar Laraba, 4 ga watan Yuli.

KARANTA KUMA  Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira Katsina yanzu, daga nan zai tafi Mauritania gobe

Add comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *