Jami’an tsaro sun gano cewa wata sabuwar ‘Darika ta bayyana a Najeriya

Mun samu labari cewa wasu Mabiya addinin Musulunci da ba a san da irin su ba sun shigo cikin Kasar nan inda su ke daukar Mabiya musamman a Arewacin kasar nan a halin yanzu.

Rundunar Sojin kasa na Najeriya ta sanar da Jami’an shige da fice na kasar nan watau NIS cewa akwai wata sabuwar Kungiyar addinin Musulunci wanda ake kira “Hakika” da ta shigo cikin Najeriya kuma ta ke daukar Mabiya a Arewa.

Shugaban Hafsun Sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai Wata takarda ta zo hannun mu daga Maiyegun Diary inda wani Jami’in Sojan kasar nan mai suna Laftana TG Iortyom ya sanar da Jami’an shige-da-ficen na Najeriya wannan bayani a madadin babban Hafsun Sojin kasar a wata wasika.

Takardar da aka aika a boye ta tabbatar da cewa an samu bayyanar wadannan Bakin Mabiya addinin Musulunci a Yankin Ngwurore da ke cikin Kudancin Garin Yola da ke Jihar Adamawa da kuma Garin Toto da ke Jihar nan ta Nasarawa.

Laftana Iortyom ya bayyana cewa bayanai sun nuna cewa wannan Kungiya tana daukar Mabiya a fadin Jihohin nan inda ta ke kira ayi watsi da sallolin yini da kuma azumin da ake yi cikin Watan Ramadana da aka sani a addinin Musulunci.

Jami’in Sojan ya nemi Ma’aikatan shiga da fice na kasar su dauki matakin da ya dace game da wadannan Bayin Allah.

Yanzu dai za a sa wa wadannan mutane ido domin lura da aikin da su ke yi gudun kar a tada wata fitina a kasar. Dazu kun ji cewa Sheikh Ahmad Gumi wanda fitaccen Malamin addini ne a kasar nan a wata doguwar hira da yayi da Jaridar Punch ya bayyana cewa Shugaban kasa Buhari ya raba kan Jama’ar kasar.

Add comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *